ABUBUWA GOMA DA BAI KAMATA MUTUM NA YI BA A ZAUREN MUHAWARA (GROUP CHAT)





Mafi yawancin mutane a yanzu sun fi amfani da manhajoji sada zumunci ko kuma na yin muhawarori win tura sakonni a cikin wayoyinsu, a maimakon amfani da hanyar da aka sani ta aikawa da karamin sako wanda aka fi sani da (SMS).
Hakika group chat ya kawo sauki wurin tura sako ga dumbin mutane a lokaci guda, domin a cikinsa bayan rubutu da muke iya turawa, za kuma mu iya tura hotuna, bidiyo wani lokaci ma har takardu ana iya turawa, da wannan dalilin nag a ya dace mu fadawa mutane abubuwa guda goma wadanda bai kamata muyi amfani da su ba a lokacin da muke mu’amala da mutane a wurin tattaunawar.
  1. Kada ka kirki zauren muhawara mai mutane dayawa.

Mafi yawan manhajoji na tura sako (messaging applications) suna bada adadin mutanen da zaka iya aikawa sako a cikin zauren muharawa (group chat). Duk da wasu suna bada damar kari da kauda ido  daga adadin da suka kayyade bai zamo dama garemu ba mu yi ta kirkiran gidaje da dakunan muhawara barkatai ba. Kasancewar a misali dandalin WhatsApp ya baka damar saka mutane 190 a matsayin mambobi ba shi ke nuna cewar sai ka saka kowa da kowa a ciki ba.
Ko da ka kirkiri wannan zaure domin ka rika sanar da wani taro ko Muhadara ko wa’azi, wani lokaci abin zai baka mamaki idan ka sanar da wani sako da kake bukatar ayi magana gamsasshiya sai ka samu wadanda ba su san muhimmancin wannan zaure ba suna iya aikawa da sakon ‘k’ ko kuma ‘okey’.
  1. Kada ka saka mutanen da baka sani ba ac ikin group chat din

Ya fi muhimmanci ka saka mutane sanannu wanda kowa a zauren muhawaran (group chat) ya sansu. Bana son in rika yin magana da kai haka kuma ba na son ka samu lambar wayata, wannan na daya daga cikin dalilin da ya sanya bai dace ka dauki duk wanda kake da su a cikin akwatin ajiyar lambobin wayarka ka saka su a cikin grouph chart ba. Kasancewar lallai duk wanda ka saka shi a chart to yana da damar ganin lambar kowa da ke ciki wanda wannan ba zai yi wa wadansu dadi ba.
  1. KADA AKYI CHARTING DA MUTUM DAYA KACAL:

Yana da kyau kasan muhimmancin yin magana da kowa da kowa a cikin  zauren muhawara (group chat) ba tare da kebance mutum guda daya ba. wurin yin maganar da ta shafe ku  biyu yafi kyau ace ku kebance  a wajan zauren muhawarar (group chat) din. Maganar da kowa a zauren yake bukatar ji ita ake yi ac ikin zauren.
  1. KADA KA KAWO ZANTUKAN DA BA MUHALLINSU BA:

Yana da kyau ga me charting ya rin ka kawo zantuka gamsassu da suka dace a inda suka kamata, shi chating ana yin shi ne da abin da ya shafi aikace aikace hadin kai, taimakon juna da dai makamantansu. Zaka ka iya fusakntar aikin da aka baka ta yadda zaka kai ga cin masa, zaka iya zama ka nutsu ta yadda zaka cin ma maufarka.
Shin ko kana tattaunawa game da abin da ya shafi makaranta ta yadda za ku kara samun jituwa a tsakaninku? Ko kuma hirar dayanku ne a kan abin da ya shafi zaman ku na karshe, duk abin da bai shafi maudu’in da aka tsara ba, bai kamata mutum ya shigo da wani magana in ba ta maudu’in ba.
  1. KADA KA TURA KARYA KO ABIN DA BAI KAMATA BA:

Idan kana chating kayi takatsantsan da zantukan daka ke rubutawa tare da tabbatar da duk abin da ka rubuta ka samo shi daga mattabbata mai inganci. Ka da neman sauki ya sa ka rika dauko ruburu daga wadansu zaurukan ko kuma shafuka kana sakawa a cikin naku zauren ba tare da ka tantance gaskiyar maganar ba.
  1. Kada karubuta banza da

Duk da shafin muhawara ya baka dama ka rubuta abin da ka ga dama, hakan  ba dama bane a gare ka kayita rubuta banza hofi ko maimata abin da wani ya fada ba. Bai kamata a rubuta abin da bai kamata a cikin wurin da aka kebance domin tattauna wadansu abubuwa mamu himmanci ba. Misali za ka ga zaure na addini ne amma sai a sako maganar kwallo, ko kuma zauren tattaunawa a kan yadda za a bunkasa harkokin lafiya sau kaga wasu suna saka magana a kan soyayya ko makamantan haka.
  1. Kada Kayi shiru

Yin shiru a lokacin da ake tattaunawa a kan abubuwa masu muhimmanci matsala ce ga mutane da yawa a cikin zaurukan, duk lokacin da aka bijiro da wani maudu’i mai muhimmancin kuma ake bukatar kowa ya fadi ra’ayinshi to yana da kyau ka fadi naka ra’ayin, domin kada a zartar da wani abu da bai kamata ba kuma ka zauna kana korafi daga baya.
  1. Kada katura kalma daya a matsayin amsa

Domin neman saukin rubutu kada ka tura rubutu kalma daya saboda za ta iya daukar ma’ana da yawa ko kuma ayi mata wata fahimta daban da abin da shi kake nufi ba.
  1. Kada ka aika da sako a lokacin da bai kamata ba 

Idan ba zaka kira mutum da safe ko da ran aba mai zai sa ka kira shi can da daddare yana bacci. Idan kasan bai dace a tura sako a lokacin da ba yini ba ko kafin lokacin bacci yayi, to kayi amfani da wannan dubara ga manhojojin tura sako.
Mutum zai iya tura sakone kawai alokacin da bai dace ba idana  abune da yashafi gaggawa wanda ya shafi rayuwan wani. Sannan kuma ka ka sake ka tura sakon da zai hana ko bata ma wani barcin shi.
  1. Fita da ga zaure da zarar an gana abin da aka bude domin shi.

Wannan shi ne abu da mutane da yawa ba su fahimta ba, lallai a na bude zaurukan ne na wani dan lokaci musamman wadanda ake bude su domin ganin an gudanar da wani gidauniya domin tallafawa wadansu jama’a ko kuma irin wanda dalibai za su bude domin ganin sun tattauna tsakaninsu. To da zarar makasudin da ya sanya aka bude wannan zauren ya kare sai kowa ya fita daga cikin wannan zaure, ma’ana sai a rufe wannan zauren domin dalilin bude shi ya riga ya kau. Idan kuma ana ganin cewar ya dace a ci gaba da yin magana akan wadansu bayanai to yana da kyau a sanar da mambobi ko kuma a rika haduna ta zahiri ba wai komai a yi shi a boye ba.\
COPIED

Post a Comment

0 Comments