HADA INSTAGRAM DA TWITTER KO SAURAN ZAURUKAN SADA ZUMUNTA

HADA INSTAGRAM DA TWITTER KO SAURAN ZAURUKAN SADA ZUMUNTA

Kamar yadda Instagram ya shahara haka kuma yake da tarin mabiya, sannan mafi yawa daga mabiyansa suna ta'ammali da zaurukan sada  zumunta kamar twitter da sauran su, balle kuma facebook wanda dama shi ne mai mallakin instagram, yayinda kusan kaso 90% na masu  account a Instagram suna yin facebook.

To bisa ga yadda ake yin post, wani yafi Bukatar yayi post a Instagram sannan yana da account da wani zauren amma sai kaga acan ba'a tattaunawa dashi.  Wannan rubutu zai fahimtar damu yadda zaka hada Instagram dinka da wasu zaurukan sada zumunta, inda duk lokaxin da kayi post a daya daga cikin zaurukan, mabiyanka na kowanne zaure zasu ga abinda kayi post hoto, bidiyo, ko rubutu.

Misali idan ka hada Instagram dinka da twitter to idan kayi rubutu a Instagram to abokanka na Twitter zasu gani, hakan idan kayi a twitter, na instagram dinka zasu gani.
Idan kana bukatar hada instagram dinka da twitter ko wani zauren sada zumunta, saika tabbatar kana da account da su, sannan saika bi wadannan matakan:-

1. Ka bude Instagram dinka, a profile dinka saika taba
2. Idan iPhone ce da kai saika tabaIdan kuma Android ce taba 
3. Saika taba Linked Accounts, sannan ka taba zauren sada zumunta da kake bukatar ka hadesu "social network to log in and link the accounts"

Kana hadesu shi kenan, aduk lokacin da ka dauki hoto, bidiyo ko rubutu daga instagram zai bayyana a wadancan shafukan. Koda kuwa zauren sada zumuntar babushi a kasarka, misali akwai dandalin muhawara na wasu kasashe kadai,kamar irinsu China zaka samu suna da zaurukan sada zumunta na yankunansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post