Bayan gabatar da mukala akan yadda zamu kare waya daga barayi, hakan
tasa wasu suka ga cewar tasu bata da wannan tsarin a setin dinta.
Awannan darasin zamu gabatar da yadda zaka kare android dinka daga
barayi ko wacce iri ce,
Kasani:- Duk
matakin da ake dauka yana yiwuwa ne ka seta tsarin kafin a dauketa,
bayan an dauke ta,idan kayi tunanin ka saita ba zaiyi ba, bazai gano
maka ba matukar kafin ta bata baka saita shi ba.
Da wannan application zai baka dama ka sarrafa wayarka idan bata
hannunka, wato idan ka tabbatar an dauke ta, akwai abubuwan da zai iyayi
da taimakonka.
Sannan shi wannan Easy finder yana aiki akan kowacce waya, matukar
tana da Java, ga wadanda suke da Java phones suna iya dauko NQ
Anti-Virus, ko Netqin Anti-Virus duka suna dauke da wannan tsari na easy
finder, haka wanda yake da Symbian shima yana iya dauko NQ Anti-Virus,
ko Netqin Anti-Virus.
I. Idan wayar taka ta, bata ko kuma wani naka ya dauki wayar ana cire
layinka zai sanar da kai cewar an canza layin dake cikin wayarka, ka
tuntuba kaji ko sacewa akayi, wannan sakon da zai turo, zai turo ne
alamba ta musamman kamar lambar yayanka ko wani daka sa lambar sa domin
ya sanar dashi abu ya faru awayarka.
II. Kana iya adana kayan cikin wayar ta hanyar tura sako zuwa wannan
sabuwar lamba da take kan wannan waya, nan take zai kwashe maka kayan ya
adana maka su a emai dinka da kayi rijista dashi.
III. Kana iya kulle ta nan take.
IV. Sannan shi easy finder zaici gaba da turo maka hoton wurin da
wayar take duk bayan minti biyu, kana iya seta shi kasa da haka, zaici
gaba da turo maka taswirar wurin (area map)
Domin ka saita shi akan wayarka kabi wadannan matakan
1. wanda yake da Android saika je Playstore ka dauko
Ga wanda yake da Windows Phone saika je Market place/Store na Windows dinka ko kuma latsa nan
Wanda yake da Java phone saika latsa nan domin ka dauko na wayarka.
2. Ka saukar da shi (install) sannan ka budeshi.
3. Zai baka allo na farko ka jira zai baka allo na gaba
4. A wannan allo zai bayyana maka, cewar karka damu idan wayarka ta
bata, zai nuna maka aikin da zai maka akan wayarka bayan ta bata ko
ansace. Anan saika latsa Get Started.
5. Zai zabin aikinsa yana da tsari na kyauta, sannan yana da tsari na
biyan kudi, kuma N100 zai dauka daga kudin cikin wayarka, domin samun
aikinsa na (Premium) Idan ka amince su dauki N100 awayarka saika latsa Yes idan kuma na kyauta kake bukata saika latsa No thanks
6. Allo na gaba saika taba tsakiyarsa wato inda hoton waya yake, nan
zaka taba, wuri mai launin kala dake tsakiyar taswira nan zaka taba.
7. A wannan matakin, zaifi kyau kayi rijista da wannan application domin
cin wata gajiyar dole saikayi rijista dashi. Saika latsa Sign In
domin rijista, domin sai kayi rijista ne Easy finder zai iya turo maka
taswjirar hoton wurin da wayarka take (area map) sannan sai kayi rijista
dashi zai iya baka dama kayi Backup na kayan cikin wayarka, sannan
saikayi rijista zaka iya shiga shafinsu na intanet domin bincikar inda
wayarka take, sannan idan babu matsala ka biya N100, bayan ka gwadashi
yayi maka.
Sannan ka latsa SIM Card Changed bayan ka latsa shi, zaka kunna shi
domin ya fara aiki, saika shigar da lambar waninka, misali kana iya sa
lambar yayanka, ko matarka ko budurwarka, ko mahaifiyarka, lallai lambar
da zaka sa ta zama ba taka bace, baka tafiya da ita, manufar wannan shi
ne ta wannan lamba za'a sanar da su cewa wayar wane ansace ta, domin
ancanza layin da yake kanta, saboda haka ga sabuwar lambar da take kan
wayarsa.
Ku kuma ta wannan lamba zaku bi kodai ku kira lambar, ko ku kaiwa
yansanda lambar, ko ku rufe wayar, ko kuma akwai sirrin da bakwa bukata
wani ya gani, nan take zaku iya goge kanta. Idan kuma manta inda take
kayi, ko kuma tana dakin ku amma bata fili saika ziyarci find.nq.com
saika latsa Sound nan take zata yi karar sauti, koda bata da chaji
zatayi karar da zaka ganta a wuri, amma idan ba batir bazata yi kara ba.