Menene Crypto Airdrop da kuma Ya yake aiki?

Menene Crypto Airdrop da kuma Ya yake aiki? 

Crypto airdrop hanya ce na kasuwanci da ake bi don fadadi kamfani, wajan raba airdrop kyautar ko kuma wanda kadanyi wani aiki da bashi da wahala.


Menene Crypto Airdrop?

Crypto airdrop hanya ce ta samun kyautar kudi a crypto daga masu kamfani, akwai hanyoyi da dama na samun wannan kyautar coins din, mafi yawancin lokaci airdrop yana samuwa ne daga kyautar cryptocurrencies (Kwandalar Kasada), amma bai zamanto dole ba, kana bukatan kasa himma da kwazo idan ba haka ba zaka iya jijjiga daga kudin da za a chaje ka na transaction, duk da haka ana dacewa sosai wurin shiga airdrop na kyauta.


 

Misalan Airdrop na Crypto

Akwai daru-ruwan airdrop da akayi a baya, ciki da airdrop na kamfanonin crypto da suka shahara, dan haka akwai misalai da yawa na airdrop a crypto. Ana yin airdrop a crypto na shekaru da dama a duniya. A 2014 ne akayi airdrop na farko. A lokacin, zaka ga kamfani crypto yakan bayarda da 50% na coins nasu a airdrop.

Kaman kanfanin da ake kira da Auroracoin, suna da coin nasu na crypto wanda aka sani da AUR. Kamfanin suna da shirin kai AUR ya zamanto (National Cryptocurrency of Iceland). Dan haka, dukkan airdrop da akayi na AUR an bayar ne way an kasan Iceland, wanda suka karbi kwatan kwacin 31.8 AUR wa kowani mutum daya.

Airdrops da dama sun kasance a bayan Auroracoin airdrop, Kaman a 2016 da 2017, Stellar Lumens (XLM) da Bitcoin Cash (BCH) sunyi airdrop na crypt, wanda sun raba ne wa wayanda suke da Bitcoin. Bitcoin Cash wato (BCH) sun bayarda BCH da a madadin kowani Bitcoin daya, kimar san a dubban daloli ne.

Daga cikin wanda suka shahara a airdrop na crypto akwai kamfanin UniSwap, wanda Governance Token nasu wato UNI sun bayar ne wa wayanda suke rike da hajarsu a (Decentralized Exchange, DEX) a shekarar 2020. Sun rabar da sama da 250,000 kowa ya samu 400 UNI, wanda ya kasance duban daloli ne wa kowani mutum, wanda garabasa idan zaka sayar UNI a lokacin.

 

Airdrop rabu da dama.

Airdrop ya rabu da dama, wanda dukkan su suna da Kama da juna wato kamfanonin crypto suna anfani da airdrop ne dan tallata hajar su don coins nasu ya samu karbuwa a wurin al’umma, misali, kamfani suna tallata hajarsu wajan bawa sabbin masu ciniki ko kuma tsofin abokan cinikin su airdrop.

Standard airdrop

Wannan tsari ne na raba wa mutane airdrop na kyauta ba tare da kayi wani aiki tukuri ba. Kawai ka bude lalita (wallet) sai ka tura wallet address naka kawai, ana kaiyade yawan kyautar airdrop da za a bayar dan haka yana bukatar ka shiga da wurin kamin agama rabarwa.

Wannan sanan niyar hanya ce domin yana da saukin yid an samun kyautar airdrop na crypto. Ana rabawa ne ba tare da nuna ban banci ba, kana iyayi amma ba zama dole ace ka samu ba.

Bounty airdrop

Da wannan tsarin, zaka samu airdrop ne bayan kadan yi wani aiyuka, aiyukan baya zama masu wahalarwa sosai kuma dalilin airdrop din yana ingata kamfanin, shi yasa sabbin kamfanoni suke yawan anfani da wannan tsarin dan inganta hajarsu.

                                 

Holder airdrop

Yadda wannan tsari yake aiki shine, ana bada wannan airdrop dine ga masu rike da wani adadi na wani coin, yawan airdrop din yana dangata ne daga snapshot da akayi, a takaitaccen lokacin, ya danganta da kwaya nawa kake dashi dakuma idan anyi snapshot na lalitar (wallet) ka, zaka tsammaci samun wani adadi na wannan airdrop din na cryptocurrency

 

Yadda zaka samu airdrop na crypto.

Zaka iya sanin airdrop mai zuwa domin kaima ayi dakai ta hanyar biciken Google ko kuma websites da dama domin sani wani airdrop ake kanyi ko kuma wanda za ayi.

Wasu website din basu cika bafan airdrop wanda za ayi nan gaba ba domin suna kokarin kare kimarsu. Wasu sukan baiyana ne idan sun gama bincike da tabbatar da sahihancin sa, yana da kyau ka bi ra’ayin kanka akan duk wani airdrop da ka gani sai ka fadada bincike a karan kanka.

Karin haske akan haka, wasu daga cikin airdrop da ake rabawa yana ta allaka ne da mutanen da suka taba aiki da wani manhaja Kaman Swap, zaka iyayin dace ba tare da ma ka sani ba, domin anfanuwa da kalan wannan tsari zaka fara aiki ne da kallan wadannan manhajar na Swap domin an gina sune akan Blockchain da kuma saukin chaji, zaka iyayin dace ka samu alkhairi sosai.

 

Ko akwa tsaro a crypto airdrop?

Ana ganin crypto a matsayin abu mai anfanuwa da cutarwa, amma bama shine matsalar ba. Masu yaudara suna anfani da hanyar airdrop suna cutar da mutane. Suma anfani da airdrop wajan kwashe kudin mutane da sace mabudan sirri (Private keys).

Ka zamanto mai kula sosai wajan yin airdrop, mu samman idan sukayi alkawarin kudi masu yawa wanda zaka ga Kaman akwai kanshin gaskiya a ciki.

Karka zamanto mai hada lalitar (wallet) ka wanda akwai dukiyar ka aciki da wasu website da basu inganta ba ko kuma baka yarda da suba kuma kar ka bawa kowa mabudan sirrin ka (Private Keys).

Masu danfara sukan turawa mutum da coin wanda zaka ga Kaman na gaske ne amma bayida wani anfani sai a kiyaye domin kar a fada komar su.

 

 


Post a Comment

0 Comments