Hukumomin Amurka sun ce tarkacen da aka samu a wani wuri da ke can ƙasan Tekun Arewacin Atalantika sun nuna cewa jirgin ruwan OceanGate na Titan mai tafiya a ƙarƙashin teku ya gamu da "mummunan bala'i".
Duk fasinjoji guda biyar da ke cikin jirgin a take suka mutu.
Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce ta ji wata ƙara da ta yi "daidai da fashewar abin" jim kaɗan bayan ɓatan jirgin a ranar Lahadin da ta wuce, yayin da ya buga nutso zuwa ƙasan teku inda karikicen jirgin ruwan Titanic suke, nisan mita 3,800.
A ƙarshe dai, an tabbatar da asarar jirgin bayan an gudanar da wani gagarumin aikin bincike a kusa da tsibirin Newfoundland na ƙasar Kanada.
Me yake faruwa idan jirgi ya fashe, ya rufta?
Wannan lamarin na nufin cewa jirgin ƙarƙashin tekun na Titan ya rufta ba zato ba tsammani.
Mai yiwuwa saboda tsananin ƙarfin ruwa a ƙarƙashin teku wanda ya matse jirgin daga waje, in ji wakilin BBC na kimiyya, Pallab Ghosh.
An yi imanin cewa Titan ya kai nisan mita 3,500 a ƙasan teku lokacin da ya ɓata ranar Lahadin da ta wuce.
Ana tunanin jirgin ya fashe ne, ya rufta ciki sakamakon tsananin ƙarfin teku, wanda zai iya yin daidai da nauyin hasumiyar Eiffel ta ƙasar Faransa, ko kuma tan 10,000, in ji Pallab Ghosh.
Idan aka samu ruftawar wani sashen jirgin har ya faɗa ciki, ƙarfin ruwan da ke waje zai rinjayi ƙarfin da ke cikin sunduƙin, abin da zai iya kwalmaɗa shi.
An ƙera jirgin ne ta yadda zai iya jurewa irin wannan ƙarfin ruwa - kuma ƙwararru a yanzu za su yi ƙoƙarin tantance abin da taƙamaimai ya faru har aka jirgin ya fashe.
Bin ƙwaƙƙwafin tarkacen jirgin da aka gano, na iya taimakawa wajen tabbatar da haka.
Idan gundarin jikin jirgin ƙarƙashin teku ya fashe, yakan rufta ciki da saurin misalin tafiyar kilomita 2,414 a cikin sa'a ɗaya - wato saurin mita 671 a cikin daƙiƙa, in ji Dave Corley, wani tsohon jami'in jirgin ƙarƙashin teku mai dakon makaman nukiliyar Amurka.
Lokacin da yake ɗauka ya gama fashewa gaba ɗaya, bai fi misalin mili-sakan ɗaya ba, wato ɗaya cikin dubu na daƙiƙa.
Ƙwaƙwalwar ɗan'adam tana mayar da martani ga faruwar wani abu a cikin misalin mili-sakan 25, wato 25 cikin dubu na daƙiƙa ɗaya, Mista Corley ya ce.
Martanin da ɗan'adam zai iya mayarwa cikin hankali ga faruwar abu - daga fahimtar lamarin zuwa aikatawa - an yi imani mafi zafin nama shi ne milli-sakan 150 a cikin dubu na daƙiƙa ɗaya.
Iskar da take cikin sunduƙin, na da haɗakar tururin haidiro-kabon (hydrocarbon) mai yawa.
Idan jirgin ya fashe, iskar tana ƙyasta wuta sannan, sai a samu tarwatsewa bayan ruftawar farko cikin sauri, a cewar Mista Corley.
Gangar jikin mutum takan rididdige kuma ta zama toka, kafin ta bi diddigar ruwa nan take.
Mene ne zai iya haifar da ruftawar jirgin Titan?
Tsohon matukin jirgin rundunar sosjojin ruwa na Birtaniya, Ryan Ramsay ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na PA cewa ɗaya daga cikin abubuwa guda biyu, na iya faruwa.
Mai yiwuwa wata ƙofa mai makullai 17 da aka yi amfani da ita wajen rufe fasinjoji a ciki ce ta samu matsala, lamarin da ka iya haifar da fashewar jirgin "saboda ruwan cikin tekun yana da ƙarfi, ko da ba a yi tafiya mai nisa ba".
Wani abin kuma shi ne, a samu matsala da jikin jirgin shi kansa, wadda ke iya haifar da sakamako irin wanda aka gani, in ji shi.
"Irin wannan lamari na iya faruwa cikin sauri, don haka ba lallai ne fasinjojin jirgin ma. su san abin da ya faru ba," in ji shi.
Ta yaya za mu san ainihin abin da ya faru da Titan?
Duk wani bincike da za a yi, mai yiwuwa ne ya mayar da hankali ga sashen waje na jikin jirgin musamman daga tsakiya, inda aka ƙera shi da abin da ake kira 'fiber carbon'.
Abubuwan da ke nutso a cikin ruwa irin wannan, yawanci akan ƙera su ne da ƙarfe mai kauri, kamar titanium. Yana da siffa mai faɗi kamar faifai, don daidaita yanayin karfin ruwan da ke waje a ɓangarorin daban-daban na jikin jirgin.
Amma don a samu damar ɗaukan fasinjoji da yawa, jikin jirgin Titan an ƙera shi ne da siffa irinta shantu.
An kuma ƙera shi da abin da ake kira fiber carbon, kuma ba a haɗa ƙarfen Titanium a ƙarshen ɓangarorinsa biyu ba.
Ƙarfen Carbon fiber yana da ƙarfi sosai. Ana amfani da shi wajen ƙera fuka-fukan jirgin sama da motocin tsere.
Amma Titan ya fuskanci ƙarfin ruwan teku da ya ninka wanda ake samu a saman teku sau 300.
Ko ƙarfin ruwan teku mai zurfi ya matse jirgin sosai har ya fi ƙarfin kayan da aka yi amfani da su wajen ƙera shi?
Ko kuma jirgin ya yi nutso fiye da kima, da har ƙarfin teku ya raunata shi?
Ɗaukar hotunan tarkacen Titan da kuma nazarin su a ɗakin gwaje-gwaje, na iya bai wa injiniyoyi damar gano ɓangaren jirgin da ya fara fashewa.
Da zarar masu bincike sun kwaso tarkacen jirgin, za su gudanar da binciken ƙwaƙwaf a kan sassan jirgin da aka ƙera da "carbon fibre". Kowane bangare za a yi masa duban tsanaki da na'urar ganin abubuwan da ido ba zai iya gani ba, ana neman alamomin tsagewa ne don a tabbatar da inda ainihin abin ya faru.
Wurin da jirgin Titanic ya nutse yana da nisan kusan kilomita 600 (mil 370) daga gaɓar tekun Newfoundland.
Jiragen ruwan bincike a kasan teku marasa matuƙa sun gano tarin tarkace guda biyu - ɗaya ya ƙunshi bayan jirgin Titan, ɗayan kuma yana ɗauke da ƙasan jirgin. Hakan na nufin sassan sun rabu da juna bayan jirgin ya fashe.
Rear Admiral John Mauger daga rundunar tsaron gaɓar tekun Amurka, da ke jagorantar binciken jirgin Titan, ya ce bazuwar tarkacen 'ya yi daidai da faruwar wani mummunan lamari'.