Zan yi aiki bisa adalci kuma zan sakawa sojoji masu ƙwazo - Janar Lagbaja




 Sabon babban hafsan sojojin ƙasan Najeriya (COAS), Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya karɓi aiki a matasayin babban hafsan sojin ƙasa na 23 inda ya yi alkawarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa adalci.


Lagabaja ya karbi aiki ne a hannun Laftanar Janar. Faruk Yahaya wanda ke kan kujerar tun watan Mayun 2021.


Ya ce burin kowanne sojan yaƙi shi ne ya samu damar zama shugaban sojojin Najeriya.


Ya kara da cewa zai yi la'akari da cancanta da aiki tuƙuru tsakanin sojoji inda ya ce zai kyautata daidai gwargwado tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen dawo da wadanda suka kauce hanya.


Lagbaja ya yaba wa tsohon babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Janar Faruk Yahaya bisa jagoranci da kuma taimaka masa wajen gudanar da aiki.


A cewarsa, a karkash jagorancin Janar Yahaya, ‘yan bindigan da suka tuba sun mika wuya fiye da yadda aka taɓa gani a baya inda ya tabbatar da cewa aikin da ya yi a ƙarƙashinsa zai taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa na babban hafsan sojin ƙasa.


Tun da farko, Laftanar-Janar Yahaya ya ce ya bar rundunar sojin Najeriya ne a matasayin da ya fi yadda ya same ta.


Ya kara da cewa rundunar ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take yi da ayyukan rashin tsaro.


Ya ce a halin yanzu masu ta-da-ƙayar-baya na cikin ruɗani a duk filayen daga, kuma ya bukaci sojoji da kada su sassauta ƙoƙarinsu.


Post a Comment

Previous Post Next Post