"Yadda na haihu a cikin mota ba tare da taimako ba"



Wannan ne yadda lauya Julia Assis ta bayyana wa abokanta haihuwar 'yarta ta biyu, wadda ta faru a São Paulo a farkon watan Disamba.


"Mata za su so haihuwa cikin gaggawa, amma babu wadda za ta so ta haihu ita kaÉ—ai, a kan hanya, a cikin mota, ba tare da taimakon likita ba," in ji ta.


Haihuwarta ta biyu ke nan, ba kamar ta farkon ba inda aka yi mata tiyata, a wannan karon ta zaɓi ta haihu da kanta.


“An haifi Eva bayan mako 39 da kwana biyar cif. Na samu kulawa sosai daga kwararrun likitoci masu, abu na farko da suka fada min shi ne haihuwa na daukar sa’o’i.

Haihuwata ta farko ta hanyar tiyata ce, amma sun shaida min cewa wannan haihuwar tawa ta biyu za ta zo cikin sauƙi saboda jikina ya riga ya saba. In ji ta.


Lokacin da na shiga É—akin haihuwa bayan na haihu a mota, sai mutane suka tafa min.


Doula ya ce "haihuwa ce irin wadda ba a taÉ“a samun irin ta ba.” Amma na ji tsoro sosai, na gigice, kuma na shiga cikin damuwa a kan 'yata da mahaifiyata, wadanda suke gefena.


Duk da cewa ba a asibiti na haihu ba, an yi rajistar jaririyar Julia kamar an haife ta ne a asibiti.


Wannan dai daya ne daga cikin wahalhalun da ake fuskanta wajen auna haƙiƙanin yawan haihuwa da ke faruwa kafin isowar dakin haihuwa a kasar Brazil - a lokuta da dama, a kan hanyar zuwa asibiti uwa ke haihuwa ba tare da taimakon kwararrun ma'aikatan lafiya ba.


Ma'aikatar Lafiya ta bayyana cewa haihuwa a asibiti ita ce mafi aminci da kuma lafiya inda bayanai suka nuna cewa ita ce zaɓin kusan kashi 98% na mata.


“Lokacin da na fara jin alamun naÆ™uda a safiyar ranar Lahadi, ciwon ya riÆ™a Æ™aruwa har zuwa ranar Litinin, ranar Talata ma haka, ciwon ya kasance tamkar ciwon mara a lokacin jinin al`ada.”


“A ranar Laraba da Alhamis, zafin bai ragu ba ko kadan, har na kasa jurewa, wajen karfe 4 na safe, zafin ya sake Æ™aruwa sosai har na kasa kwanciya, sai na je ban-É—aki, a nan sai na ji alamun kamar ruwa ya kusa fashewa, sai na shiga bahon wanka ko zafin da nake ji zai ragu.”


“Kashe-gari sai na je asibiti, wajen likita saboda ya duba ni, da ya duba sai ya ce ruwan haihuwa ya kusan fashewa amma akwai sauran lokaci, ya ce na koma gida, bayan na koma, sai ciwon naÆ™udar ya Æ™aru sosai, ya riÆ™a taso min duk bayan minti goma zuwa ashirin.


Lokacin haihuwa, ana iya samun jaririn ya zo a juye, a lokacin da buÉ—ewar bakin mahaifa ya kai fadin 'sentimita' huÉ—u, wannan lokacin zai yi kai wa tsawon kwanaki, daga nan kuma sai lokacin haihuwar inda jariri zai fito, in ji likita Ricardo Porto Tedesco.


Abin da ake nufi a nan shi ne, tsawon naƙuda ya danganta ga yanayin ko wace mace.


Likita Ricardo Tedesco ya ce naƙuda na iya farawa a lokacin da ƙofar mahaifa ta buɗe zuwa santimita biyar ko fiye da haka, ko kuma lokacin da ciwon naƙuda ke tashi sau uku a cikin minti goma.


A lamarin Julia, tsoron yin tiyatan ya sa lamarinta ya sha banban.


“Tunda farka ina son zuwa asitibi da wuri, tun a lokacin ma da na fara jin alamun zafin naÆ™uda, amma aka ce min da na jira har lokacin haihuwar a yi idan ba haka ba kuma idan na je, tiyata za su iya mun.” In ji ta


“Da karfe 1:37pm, na ji kamar ruwa haihuwa na zai fashe kuma dama an yanke shawarar nurse ne zai zo har gida ya duba ni kafin lokacin haihuwar tayi, amma hakan bai yiwu ba saboda wajen su da nia daga gida na.”


“Da karfe 2pm, ina cikin bahon wanka yanda liklta ya ce min nayi, ni kadai duk da dai miji na da mahaifiyata suna nan, zafin naÆ™udar sai Æ™aruwa yake yi tare da alamun ruwan haihuwan ya kusan fashewa.”


“Toh, karfe 2:30 na kasa jurewa zafin, kawai sai na fara ihu ina kuka har nurse din ya jiyo ta waya, shine ya ce ayi maza a kai ni asibiti.


“A hanyar zuwa asibiti, a cikin mota, sai na fara jin alamun jaririn na cuso kai har yayi alamun fitowa, sai na fadawa mahaifiyata, shine a firgice ta saka hannu don ta taro jaririn, muna shiga É“angaren haihuwa da motar, kawai sai jaririn ya fito”


“Da aka bude motar, da kaina na sauka, har na taka na zauna akan gujerar da ake tura marasa lafiya, tare ta jaririyata a hannu na, mahaifiyata kuma duk fuskar ta na dauke da tsoro da gigicewa, sai na riÆ™i wasu su kulan min da ita.


A cikin asibiti, sa'o'i kadan bayan haihuwar, likitocin sun gano cewa Julia na fama da zubar jini wanda. Sai da aka yi mata ƙarin jini biyu, amma ta warke cikin mako guda.


HaÉ—urra

A cewar masana, haihuwa na musamman waÉ—anda mata ke yi a hanya ksfin isa asibiti suna da irin wannan haÉ—ari:


- Za a iya samun rashin iya lura da sabon jariri ko yiwuwar rikicewa a cikin uwa;


- Za a iya samun haɗarin rauni - jaririn na iya faɗi ƙasa ko kuma da wuya ya iya samun tallafi a lokacin da ya fito daga ciki.


Game da haihuwar inda ba taimakon likita ko nurse, za a kuma iya samun hadarin wahala ga jaririn idan naƙudar ta yi yawa a cewar Ricardo Tedesco.


"A cikin waɗannan wani yanayi kuma inda ake buƙatar oxygen zuwa mahaifa, za iya wahala a samu.


“Za a kuma iya samun HaÉ—arin wanda zai iya haifar da zubar jini.”


Mene ne ya kamata a yi idan haihuwa ta zo babu ƙwararren da zai taimaka?

Abu mafi mahimmanci shine tabbatar da yara yana cikin dumi, a cewar likita Ana Cris Duarte.


"Ya na da kyau a sami tawul don nannade jariri. Sannan kuma za a iya É—ora jaririn a jikin mahaifiyarsa, fata da fata, a rufe jiki da kyau, sannan ku je asibiti, neman taimako, wannan shi ne babban abu, "in ji shi.


"Ba sai an yanke cibiyar jaririn ba, ba sai an cire mahaifa ba, na ga wasu mutane ma suna É—aure cibiyar jariri da igiyar takalmi, ba sai an yi ko daya daga wadannan ba" in ji Likitan


Ya na da matuƙar mahimmanci a nemi taimakon gaggawa don tabbatar da cewa uwa da yaro suna lafiya.


“Kusan kashi 5% na jarirai suna bukatar taimako wajen numfashi a lokacin haihuwa, Har ila yau, zubar jini bayan haihuwa na iya faruwa.


Post a Comment

Previous Post Next Post